14 Faburairu 2021 - 14:03
Iraki:Mayakan Kungiyar Daesh 21 Ne Suka Halaka A Lardin Samira

Kwamandan rundunar sojojin kasar Iraki a Lardin Samira ya bada sanarwan halakar mayakan kungiyar ‘yan Ta’adda ta Daesh 21 a lardin.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran ‘Shafaq News’ ya nakalto Jabbar Addarraji kwamandan rundunar, ya na fadar haka a safiyar yau Asabar. Ya kuma kara da cewa wani dan kunan bakin wake ne daga cikin mayakan kungiyar ya makare motarsa da boma bomai da nufin kai harin kunan bakin wake a cikin gari, sai ya yi kuskure ya latsa hon din motarsa, wanda yake hade da boma-boman. Sai suka tashi suka halakasu gaba daya.

Tun shekara ta 2017 sojojin kasar ta Iraki ta re da mayakan sa kai na kungiyar Hashdushabi suka kawo karshen ikon kungiyar ta Daesh a arewacin kasar ta Iraki, amma har yanzun akwai daddaikun ‘ya’yan kungiyar wadanda suke kai hare-haren sari ka noke, ko na kunan bakin wake a kan jami’an tsaro da mutanen kasar nan da can.

342/